<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><hymn_number>126</hymn_number>
<title>Ku Duba Irin Ƙaunan Nan, Ƙauna Ta Allahnmu LW126</title>
<lyrics>[V1]
 1) Ku duba irin ƙaunan nan, ƙauna ta Allahnmu,
 Domin mu zama ƴaƴansa, ya dinga ƙaunarmu.

[V2]
 2) I, domin wannan, duniyan nan ta riƙa raina mu,
 Wahalarmu fa ɗaya ce da ta Ubangiji.

[V3]
 3) Yanzu mu ƴaƴan Allah ne, a cikin duniyan nan.
 A rufe ya ke tukuna, zama na Sama can.
 4) Mun sani ran da shi zai zo, ma zama kamarsa, Zai buɗe mana idanu, mu ga jamalinsa.

[V4]
 5) Wanda ya ke da begen nan kafe a bisansa.
 Zai tsare tasa zuciya kamar Mai Cetonsa.</lyrics>
</song>